Isa ga babban shafi
Afirika

Amurka ta kaddamar da hari kan mayakan IS a Sirte

A karon farko jiragen yakin kasar Amurka sun yi luguden wuta a yankunan dake hannun mayakan IS da suka ja tunga a birnin Sirte na kasar Libiya.

Mayakan sa kai a Libiya
Mayakan sa kai a Libiya
Talla

Prime Ministan Libiya mai samun goyon bayan majalisar dinkin duniya Fayez al-Sarraj ya ce harin jiragen yakin Amurka ya kashe da yawa daga cikin mayakan na IS.

Kasar Amurka dai ta ce ta kaddamar da kai hare-haren saboda bukatar hakan da gwamnatin Libiyan ta yi ta hannun rundunar sojin kasar.

Sojin Libiya sun yanke shawarar neman taimakon Amurka saboda kasa kutsawa da suka yi cikin birnin na Sirte kasancewar mayakan na IS sun dasa nakiyoyi a duk wata hanyar shiga cikin birnin.

Wata majiya daga rundunar sojin Libiyan ta ce luguden wutar da jiragen yakin suke yi zai taimaka wajen share musu hanyar da za su samu damar dannawa cikin birnin da nufin kakkabe mayakan na IS.

Idan har birnin Sirte ya kubuce daga hannun mayakan IS hakan zai jawo musu koma baya a kokarin da suke na mamaye kasar Libiya.

Wata majiyar kiwon lafiya a kasar ta ce kawo yanzu sojin gwamnati 280 suka rasa rayukansu, yayinda 1,500 suka samu munanan raunuka tun bayan da rundunar sojin kasar ta kaddamar da kokarin kwace birnin na Sirte daga hannun mayakan IS.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.