Isa ga babban shafi
Najeriya

APC ta gayyaci Jibrin kan badakalar kasafin kudi

Jam’iyyar APC mai mulki a Najeriya ta bukaci Hon Abdulmumin Jibrin ya gurfana gaban kwamitin da’a na Jam’iyyar a yau Talata kan tonon sililin da ya ke na cuwa-cuwar da shugabannin majalisar wakilai suka yi a kasafin kudi na 2016.

Abdulmumin Jibrin ya fasa kwai a Majalisar Wakilai bayan tube shi shugaban kwamitin kasafin kudi
Abdulmumin Jibrin ya fasa kwai a Majalisar Wakilai bayan tube shi shugaban kwamitin kasafin kudi channelsyoutube
Talla

Hon Jibrin dai tsohon shugaban kwamitin kula da kasafin kudi ne a majalisar wakilai kuma bayan tube shi ne ya fara bankado cuwa-cuwar da ‘Yan Majalisar suka yi na karin kudade a wasu ayyuka na kashin kansu a kasafin kudin bana.

Jam’iyyar APC kuma na neman shiga tsakanin Dan Majalisar da kuma Shugabannin Majalisar.

A wasikar da ta aikawa Jibrin, Jam’iyyar APC ta ja kunnen shi na shiga kafafen yada labarai ba tare da yin tunani ba.

Abdulmumin Jibrin ya ce, ya aike da wasika ga hukumomin yaki da cin hanci da rashawa don gudanar da bincike kan zargin da ya ke yi wa bangaren shugabancin Majalisar.

Jibrin na zargin shugaban majalisar Yakubu Dogara da mataimakinsa Yusuf Lasun da wasu kusoshin majalisar guda biyu da cin amana da kuma yunkurin shigar da cuwa-cuwa a kasafin kudin shekarar 2016, lamarin da ya haifar da cece-kuce a fadin kasar.

Amma Jam’iyyar APC ta ce kundinta ya tanadi hanyoyin warware duk wani sabani tsakanin ‘ya’yanta tare da daukar matakai akan duk wani dan Majalisa da kokarin lalata sunan Jam’iyyar.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.