Isa ga babban shafi
Afrika ta tsakiya

CAR: Za a soma tattaunawa da ‘Yan tawaye

Shugaban Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya Faustin-Archange Touadera ya ce zai fara tattaunawa da shugabannin kungiyoyin da ke dauke da makamai a kasar da nufin kwance damara da kuma samarwa tsoffin ‘yan tawaye ayyukan yi.

Faustin-Archange Touadéra Shugaban Jamhuriyyar Afrika ta tsakiya
Faustin-Archange Touadéra Shugaban Jamhuriyyar Afrika ta tsakiya © ISSOUF SANOGO / AFP
Talla

Sanarwar hakan ta zo ne kwana guda bayan da kasar ta samu tallafin kudade CFA bilyan 4 daga kasashen yankin tsakiyar Afirka domin sake gina kasar da kuma kwancewa ‘yan tawaye damara.

A karshen taron da suka gudanar a Lahadi a birnin Malabo na Eqautorial Guinea, kasashen Kamaru da Congo da Gabon da kuma Equatorial Guinea, kowace ta amince ta taimaka da CFA bilyan daya.

Ana dai ci gaba da samun tashin hankali bayan rantsar da shugaban kasar Faustin-Archange Touadera a matsayin shugaban kasa.

Amma shugaban ya ce gwamnatin shi za ta yi kokarin bin matakan da suka dace domin ‘yanto kasar tare da taimakon dakarun kasashen Faransa da na Afrika da wasu kasashen duniya da ke aikin wanzar da zaman lafiya a Bangui.

Jamhuriyyar Afrika ta tsakiya ta fada cikin rikici tun a watan Maris din 2013 bayan mayakan Seleka musulmi sun hambarar da gwamnatin Francois Bozize, Kirista.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.