Isa ga babban shafi
Afrika ta Kudu

Pistorious na iya kashe kanshi a gidan yari

Rahotanni daga kasar Afrika ta kudu sun ce yanzu haka an sanya Oscar Pistorius a karkashin kyakkyawar kulawa a daidai lokacin da ake fargabar cewa zai iya kashe kansa a gidan yarin da ake tsare da shi saboda kashe budurwarsa Reeva Steenkamp.

Pistorious a kotu lokacin sha'ri'ar kashe budurwarsa Reeva Steenkamp
Pistorious a kotu lokacin sha'ri'ar kashe budurwarsa Reeva Steenkamp REUTERS/Siphiwe Sibeko
Talla

Hukumomin gidan yari sun tabbatarwa jaridar City Press cewa, tsohon zakaran tseren gudun nakassun wanda ke zaman gidan yari na shekaru shida, ana sa masa ido sosai bisa fargabar cewa zai iya kashe kansa a koda yaushe.

A makon da ya gabata ne aka gano Pistorious ya sami rauni a hannu ana kuma zargin dan wasan ya jiwa kansa ciwon ne da gangan duk da cewa ya musanta hakan.

Shekaru uku da suka gabata ne Oscar Pistorious ya harbe budurwarsa Reeva Steenkamp har lahira, yanzu yana zaman gidan yari na tsawon shekaru 6.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.