Kungiyar Alkalan Nijar ta soki Issoufou
Kungiyar alkalai SAMAN a Jamhuriyar Nijar ta zargi shugaban kasar Issoufou Mahamadou da kokarin tauye ‘yancin da kundin tsarin mulkin kasar ya bai wa bangaren shari’a, saboda yadda shugaban ke canzawa alkalai wuraren aiki ba tare da an bi ka’ida ba.
Wallafawa ranar:
A zantawarsa da RFI Hausa, Mataimakin shugaban kungiyar alkalan Nouhou Boubakar, ya ce Shugaba Issoufou na nada wadanda ya ke da alakar siyasa da su ba tare da la’akari da kwarewar aikin shari’a ba.
Kungiyar Alkalan ta soki Issoufou ne kan nada wani Dan Jam’iyyarsa ta PNDS Tarayya a matsayin alkalin wata babbar Kotun da ke kula da dukiyar kasa wato Cour des Comptes.
Alakalan na ganin nada dan siyasa mataki ne da zai janyo rikici da tabbatar da rashin adalci ga aikin tafiyar da babbar kotun.
Sannan Kungiyar ta ce kundin tsarin mulkin Nijar ya haramta hada siyasa da ‘yancin aikin Shari’a.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu