Isa ga babban shafi
Mali

Mayakan jihadi sun karbe wani gari a Mali

Mayakan jihadi sun kwace garin Boni da ke tsakiyar kasar Mali, bayan sun kaddamar da hari kan wasu gine-ginen gwamnati tare da fatattakar sojojin da ke tsaron yankin.

Mayakan jihadi sun karbe iko da garin Boni da ke kasar Mali
Mayakan jihadi sun karbe iko da garin Boni da ke kasar Mali AFP PHOTO / ROMARIC OLLO HIEN
Talla

Wani zabebben jami’in gwamnatin kasar da ya bukaci a sakaya sunansa da kuma wata majiyar tsoro, sun tabbatar wa kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP da wannan rahoton, inda suka ce a halin yanzu mayakan na rike da ikon garin na Boni.

Majiyoyin sun ce, a wannan ranar ta jumma’a ne mayakan suka kusta kai cikin garin, inda suka yi ta harbe-harben bindiga a sararin samaniya, yayin da kuma suka kona ofishin magajin garin da kuma gidan shugaban ‘yan sandan kasar.

Rundunar sojin kasar ta bukaci jami’anta da su fice daga garin don neman mafaka a garin Douentza mai tazarar kilomita 90 daga Bonin.

Tuni dai gwamnatin kasar ta alakanta harin da ta'addanci, yayin da kungiyar Ansar Dine da wata sabuwar kungiyar gungun kabilu, duk kowannensu ta yi ikirarin kai farmakin.

A watan Janairun shekara ta 2013 ne aka girke dakarun kasashen waje a Malin, abinda ya taka rawa wajen fatattakar mayakan daga manyan garuruwan kasar.

Sai har yanzu, akwai yankunan da ba sa karkashin ikon dakarun.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.