Zanga zanga ta rikide zuwa tarzoma a Zimbabwe
Shugaba Robert Mugabe yayi kaukausar suka kan alkalan kasar da suka baiwa ‘yan adawa izinin gudanar da zanga zangar da ya rikide zuwa tarzoma.
Wallafawa ranar:
Shugaba Mugabe wanda ya bayyana alkalan a matsayin marasa hankali yace yana fatan sun fahimci illar da suka yi ganin yadda masu zanga zangar suka tada hankalin jama’a.
Tabarbarewar tattalin arziki da rashin aikin yi musanman a tsakanin matasan kasar na daga cikin dalilan da suka harzuka 'yan adawa gudanar da zanga zangar.
‘Yan adawar sun samu izinin zanga zanga ranar 26 ga watan jiya wadda ta haifar da arangama tsakaninsu da ‘Yan Sanda, al’amarin ya kaiga kama 70 daga cikin su.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu