Isa ga babban shafi
Kenya

Manoman Afrika za su ci gaciyar biliyoyin Dala

Manoman Afrika za su ci gaciyar biliyoyin Dala da aka yi musu alkawari a wani taro da aka gudanar a birnin Nairobi na Kenya.

Manoman Afrika za su ci gaciyar biliyoyin Dala
Manoman Afrika za su ci gaciyar biliyoyin Dala Reuters
Talla

Shugabannin Afrika da kungiyoyin agaji na duniya da kamfanoni masu zaman kansu na cikin wadan da suka yi alkawarin don habbaka harkar noma a Nahiyar.

Wadanda suka yi alkawarin bayar da makudan kudadden sun hada da shugabannin Afrika da bankin raya kasashen na Afrika da kuma kamfanoni masu zaman kansu har ma da wasu kungiyoiyin agaji daga kasashen ketare.

Kawo yanzu dai an bada himmar samar da dala biliyan 30 a taron gwagawrmayar kare muhalli da aka gudanar cikin wannan makon a birnin Nairobi na kasar Kenya.

Wanan adadi na kudi dai shi ne mafi girma da bangaren noma a Afrika zai samu , kuma ana saran kudin zai taimaka wajen habbaka harkar ta noma cikin shekaru 10 masu zuwa.

Shugaban Kenya, Uhuru Kenyatta ya yi alkawarn bayar da dala miliyan 200 don taimaka manoman yayin da ya kalubalanci takwarorinsa na Afrika da su gaggauta zuba jari a harkar noman don amfanin nahiyar.

Shi kuwa shugaban bankin raya kasashen Afrika, Akinwumi Adesina, cewa ya yi, yana son Afrika ta ciyar da kanta da kuma bunkasa cikin alfahari.

Itama dai gidauniyar Bill and Melinda za ta ajiye zunzurutun Dala biiliyan 5 don wanann taimako.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.