Isa ga babban shafi
Zimbabwe

An girke jami'an tsaro saboda 'yan adawar Zimbabwe

Gwamnatin Zimbabwe za ta girke jami’an kwantar da tarzoma bayan ‘yan adawar kasar sun yi shirin gudanar da zanga-zanga a yau Asabar, don neman shugaba Robert Mugabe yin murabus daga mukaminsa.

Ana zargin shugaba Robert Mugabe da murkushe 'yan adawar Zimbabwe bayan sun nuna adawa da zarcwarsa kan karagar mulki
Ana zargin shugaba Robert Mugabe da murkushe 'yan adawar Zimbabwe bayan sun nuna adawa da zarcwarsa kan karagar mulki REUTERS/Philimon Bulawayo
Talla

A cikin makon daya gabata ne, hukumomin kasar suka haramta gudanar da zanga-zanga a birnin Harare, amma masu gangamin suka lashi takobin kalubalantar haramcin a kotu.

Gungun jam’iyyun adawar kasar dai, na bukatar a sauya tsarin gudanar da zabe gabanin zaben shekarar 2018, inda shugaba Mugabe mai shekaru 92 ke shirin sake tsayawa takara.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.