Isa ga babban shafi
Jamhuriyyar Congo

Yajin aikin ‘Yan adawa ya yi tasiri a DR Congo

Rahotanni daga Jamhuriyar Dimokiradiyar Congo sun ce harkokin yau da kullum sun tsaya cak a Kinshasa babban birnin kasar sakamakon yajin aikin gama da gari da ‘Yan adawa suka kira don kalubalantar dage zaben shugaban kasar zuwa shekarar 2018.

Yajin aikin 'yan adawar Congo ya yi tasiri
Yajin aikin 'yan adawar Congo ya yi tasiri Sonia Rolley/RFI
Talla

Sakatare Janar na Jam’iyyar UDPS Jean-Marc Kabund ya ce yajin somin tabi ne kan shirin da suke na hana shugaba Joseph Kabila kara koda kwana guda bayan wa’adin mulkinsa ya cika daga ranar 19 ga watan Disamba.

Kaddamar da Yajin aikin na zuwa ne bayan sanya hannu kan wata yarjejeniya tsakanin shugaba Kabila da wani bangare na ‘Yan adawa da suka amince ya yi tazarce

Tuni kasashen duniya musamman Faransa da Amurka suka soki shirin dage zaben da kuma takarar Joseph Kabila.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.