Isa ga babban shafi
Kenya

Tashin Bam ya halaka mutane 12 a Kenya

‘Yan Sanda a kasar Kenya sun ce mutane 12 suka mutu sakamakon wani harin bam da aka kai a arewa maso gabashin kasar.

Harin da aka kai kan ginin gwamnati a arewa maso gabashin Kenya
Harin da aka kai kan ginin gwamnati a arewa maso gabashin Kenya
Talla

‘Yan Sandan sun ce an kai harin ne wani gidan gwamnati.

Shugaban ‘yan sandan yankin, Job Boronjo ya tabbatar a yawan wadanda suka rasa rayukansu a harin, wadanda suka kunshi maza 11 da kuma mace daya.

Kasar Kenya na fama da hare haren ta’addanci daga yan kungiyar Al Shebaab dake kasar Somalia tun bayan da sojojin Kenyan suka kutsa kai kasar dan tallafawa gwamnati.

A watan Nuwamban shekara ta 2013 mayakan al Shabaab sun yi sanadin mutuwar fararen hula 67 a wani ginin saida kayayyaki da ke Nairobi.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.