Isa ga babban shafi
Faransa-Afrika-Turai

Manuel Valls zai gana da wasu Shugabanin Afrika

Firaministan kasar Faransa Manuel Valls ya samu isa kasar Togo, masomin wata ziyarar kasashen yammacin nahiyar Afrika, da suka hada da Togo, Ghana da kuma kasar Cote d’Ivoire wata alamar tabbatar da goyon bayan Fransa kan yadda demokradiyar kasashen ke tafiya, tare da mutunta dokokin duniya.

Manuel Valls Firaministan kasar Faransa
Manuel Valls Firaministan kasar Faransa GUILLAUME SOUVANT / AFP
Talla

Bayan ganawa da Shugaban kasar Chadi da jamhuriyar Niger a shekara ta 2014, da kuma Mali da Burkina Faso a 2015, sai watan Satumba na shekara 2016 da ya gabata kuma ya sauka a Senegal,
yanzu haka da Manuel Valls na ci gaba da ziyarar kasashen yankin Sahel, da ya fada cikin barazanar ayyukan ta’addanci.

Mista Valls, da zai iya kasancewa dan takarar shugabancin kasar Fransa a 2017 a karkashin inuwar jam’iyyar yan gurguzu, idan shugaban kasar mai barin gado Francois Hollande ya ki ya sake tsayawa takarar neman kujerar shugabancin kasar a karo na 2,

Majiya daga mukaraban sa a wannan zagaye ta ce babban makasudin ziyarar ta Firaministan Faransa Valls ita ce nuna goyon baya ga demokradiyar kasashen na yammacin afrika.

Manuel Valls zai ziyarci kasashe da suka hada da Togo a yau juma’a, gobe assabar Ghana sai kuma ya kammala da Côte d'Ivoire.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.