Isa ga babban shafi
Congo

Yan adawa a kasar Congo sun halarci gangamin da aka haramta.

A safiyar yau assabar dadadden dan adawar nan na kasar Jamhuriyar Dmokradiyar Congo Etienne Tshisekedi, ya yi niyar yi wa magoya bayansa jawabi a wani taron gangami da ya kira a birnin kinshasa babban birnin kasar.

Taron gangamin yan adawar kasar Jamhuriyar Demokradiyar Congo
Taron gangamin yan adawar kasar Jamhuriyar Demokradiyar Congo RFI/Sonia Rolley
Talla

Taron gangamin da gungun yan dawa suka lashi takobin halarta, duk kuwa haramcin da mahukumta suka yi kan yin sa.

Rundunar Majalisar Dinkin Duniya a kasar ta Congo ta bayyana kara daukar matakan tsaro a yau assabar, a lungu da sakon birnin Kinshasa, domin tabatar da ganin an mutunta yanayin tsaron lafiya da dukiyoyin al’umma

Mahukuntan kinshasa dai sun cire layin watsa shirye shiryen Radiyo France Internationale ta zangon FM a birnin.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.