Isa ga babban shafi
Jamus

Jamus ta kara wa Afrika kudaden tallafi

Kasar Jamus ta sanar da kara yawan agajin da ta ke ba kasashen Afirka ta hannun Majalisar Dinkin Duniya zuwa euro miliyan 61 domin ganin sun dauki matakan hana ‘Yan kasashensu kwarara zuwa Turai.

Dubban 'Yan ci rani ke mutuwa a tekun Bahrum
Dubban 'Yan ci rani ke mutuwa a tekun Bahrum RFI/Juliette Gheerbrant
Talla

Karin ya nuna cewar Jamus za ta bayar da euro miliyan 298 a bana ga hukumar kula da ‘Yan gudun hijira.

Minsitan harkokin wajen Jamus Frank-Walter Steinmeier ya bayyana shirin kara yawan kudin agajin a ganawar da suka yi da kwamishinan ‘Yan gudun hijira Fillippo Grandi a Berlin.

Kasashen da Jamus ta ke sa ran za su amfana da kudin sun kunshi wadanda ke fama da tashe tashen hankula da masu fama da talauci da kuma fari, wadanda ‘yan kasar su ke tserewa zuwa Turai ta teku mai dauke da hatsari.

Minista Steinmeier ya ce kasashen da ke fama da irin wadanann matsaloli na bukatar taimako, saboda haka kudaden za su taka rawa wajen tallafa musu.

Akalla baki sama da miliyan daya daga Afirka da Asia da kuma Gabas Ta Tsakiya ne suka shiga turai bara, yayin da dubbai suka mutu a cikin teku.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.