Isa ga babban shafi
Saliyo

Amnesty ta bukaci janye dokar hana ‘yan mata masu ciki yin karatu

Kungiyar kare hakkin dan Adam ta Amnesty International ta bukaci hukumomin kasar Saliyo da su janye dokar haramta wa ‘yan mata da ke da juna biyu zuwa makaranta.

Moiyattu Banya shugaban kungiyar dake fafutukar kare 'yan cin mata a Saliyo tare da wasu 'yan mata.
Moiyattu Banya shugaban kungiyar dake fafutukar kare 'yan cin mata a Saliyo tare da wasu 'yan mata. AminAmeen Photography
Talla

A cikin wata sanarwa da ta fitar, Amnesty International ta ce, wannan dokar dai na ci gaba da nuna banbancin jinsi tsakanin maza da mata a kasar ta Saliyo, lamarin da ke barazana ga makomar ilimin dubban ‘yan mata nan gaba.

Darektan kungiyar a yankin yammaci da kuma tsakiyar Afrika, Alioune Tine ya ce, haramcin zuwa makarantar kuskure ne, kuma hakan ba zai magance matsalar daukan ciki tsakanin ‘yan mata masu kananan shekaru ko marasa mijin aure a kasar ba.

Tine ya kara da cewa, matsalar ta daukan ciki ta tsananta ne bayan annobar cutar Ebola da ta afkawa kasar, in da kididdiga ta nuna cewa fiye da ‘yan mata dubu 18 ne suka yi ciki a lokacin barkewar annobar, yayin da dokar ta shafi ‘yan mata dubu 10 a bara.

Mr. Tine ya bukaci hukumomin Saliyo da su kara kaimi wajen wayar da kawunan matan a fannin saduwa a maimakon daukan matakin haramta musu zuwa makaranta.

Tun kafin bayyana cutar Ebola, kasar ta Saliyo na da kashi 28 cikin 100 na ‘yan mata masu shakaru 15-19 da ke daukar ciki ba tare da mijin aure ba a duniya.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.