Isa ga babban shafi
Uganda

ICC za ta fara shari'ar Ongwen na Uganda

Kotun hukunta manyan laifufuka ta duniya da ke Hague za ta fara shari’ar mataimakin shugaban kungiyar ‘yan tawayen LRA da ke Uganda Dominic Ongwen, wanda ake zargi da hannu wajen kisan mutane sama da dubu 4.

Dominic Ongwen, mataimakin shugaban kungiyar LRA ta Uganda
Dominic Ongwen, mataimakin shugaban kungiyar LRA ta Uganda © REUTERS/Michael Kooren
Talla

A wannan Talatar ne za a fara yi wa Ongwen da ya haura shekaru 40 shari’ar, kuma zai kasance mutun na farko da kotun za ta fara gurfanarwa daga cikin mayakan Lord Resistance Army. 

Duk da cewa an kafa kungiyar ne a kasar Uganda, to sai dai ana zargin mayakanta da aikata laifufukan yaki a kasashe makota, da suka hada da Jamhuriyar Dimokuradiyyar Congo da kuma jamhuriyar Afrika ta Tsakiya.

Kazalika ana zargin mayakan karkashin jagorancin Joseph Kony da aikata laifukan yaki har guda 70 da suka hada da kona gidajen jama'a da yi wa mata fyade da kuma cin zarafin kananan yara.

A bangare guda, Majalisar Dinkin Duniya ta zargi kungiyar ta LRA da kashe mutane sama da dubu 100 tare da sace kananan yara har dubu 60 tun bayan da ta yi wa gwamnatin Kampala tawaye.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.