An gwabza kazamin rikici a Baminda da ke Kamaru
Akalla mutane biyu aka tabbatar da mutuwar su a rikicin da ya barke tsakanin ‘yan sanda da masu zanga-zanga a yankin masu amfani da harshan Ingilishi na Baminda da ke arewa maso kudancin Kamaru.
Wallafawa ranar:
Rahotanni da kafafan yadda labaran talabijin din kasar ke tabbatarwa, ya ce kungiyar matasa yankin ta yi kokarin hana zaman tattaunawar Jami’iyyar PDM, ta shugaba mai ci Paul Piya a Baminda, wanda ya haifar da hargitsin da ‘yansanda sukayi harbi.
Sai dai kakakin jam’iyyar adawa ta SDF, Denis Nkemlemo, ya ce wadanda suka mutu sun kai 4.
Sama da wata guda kenan da kungiyar lauyoyi, malaman makarantu da sauran ma’aikata da ke wannan yanki ke gangami nuna adawa da tauye musu hakokinsu.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu