An dawo da dokar hana fita a wasu yankunan Kaduna
Gwamantin Jihar Kaduna ta dawo da dokar hana fita a kananan hukumomin da ke fama da rikici a kudancin jihar bayan sassauta dokar saboda bukukuwan Kirsimeti.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
An dai sassauta dokar daga sa’o’I 24 zuwa 12 domin bai wa jama’a damar gudanar da bukukuwan kirismeti a cikin sauki. Amma dokar za ta ci gaba da aiki sakamakon hare-hare da ake fuskanta a yankunan.
Samuel Aruwan da ke magana da yawun gwamnan Jihar ya shaidawa RFI Hausa cewa daga yau Talata dokar za ta koma ta tsawon sa’o’I 24 a kananan hukumomin jihar guda uku wato Jema’a da Kaura da kuma Kataf.
An samu salwantar rayuka sakamakon rikici tsakanin makiyaya da wasu kabilun yankin na kudancin kaduna.
Rahoton Aminu Sani Sadu daga Kaduna
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu