Isa ga babban shafi
Mali

An bude taron Faransa da kasashen Afrika 30 a Mali

Shugabannin kasashen Afrika 30 na gudanar da taro tare da Faransa a birnin Bamako na Mali a yau Juma’a inda za su tattauna yaki da ta’addanci da kuma hanyoyin inganta dimokuradiya a tsawon kwanaki biyu.

Harabar dakin Taron kasashen Afrika 30 da Faransa a Bamako na Mali
Harabar dakin Taron kasashen Afrika 30 da Faransa a Bamako na Mali RFI/Paulina Zidi
Talla

Ana sa ran taron ya tattauna batun rikicin siyasar Gambia, inda shugaban kasar Yahya Jammeh ke son ci gaba da mulki bayan ya sha kaye a zabe a watan Disemba. Haka ma taron zai tabo batun Joseph Kabila na Congo da ya ki amincewa ya sauka bayan cikar wa’adin shi.

Taron kuma zai ya tabo batun matsalar ‘Yan ci-rani inda ‘Yan Afrika ke tsallakawa zuwa Turai.

Yawancin kasashen da suka halarci taron wadanda Faransa ne ta yi wa mulkin mallaka da kuma ta ke ba taimakon tsaro. Akwai kuma kasashe masu magana da Ingilishi da suka halarci taron.

Faransa dai na horar da sojojin kasashen Afrika sama da 20,000 duk shekara domin kakkabe barazanar ‘Yan ta’adda. Manufar Faransa kuma ita ce rage turo sojojinta ga aikin wanzar da tsaro ga kasashen da ke fama da rikici.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.