Boko Haram : Mata sun fara kai hari da goyo
Hukumar agajin gaggawa a Najeriya NEMA, ta ce wata mata da ta kai harin kunar bakin wake a Madagali da ke cikin Jihar Adamawa a arewacin kasar tana dauke ne da goyo a lokacin da ta kai harin.
Wallafawa ranar:
Jagoran Hukumar NEMA a Jihar Adamawa Saad Bello wanda ya tabbatar da Matar na dauke da goyo a lokacin da ta kai harin a Madagali, ya ce ga alama wannan wani sabon salo ne da kungiyar Boko Haram ta fara amfani da shi domin kai hare-harenta.
Akalla mutane biyu suka mutu sannan 15 suka jikkata a harin wanda aka kai a wani shingen binciken sojoji da ke kusa da tashar shiga mota a Madagali a ranar 13 ga Janairu.
Boko Haram dai ta dade tana amfani da Mata da Kananan yara a hare haren kunar bakin waken da ta ke kai wa a makarantu da kasuwa da wuraren ibada da kuma jami'an tsaro.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu