Isa ga babban shafi
Botshuwana

A Botshuwana Jam'iyun adawa 4 sun hade don yakar jamiya dake mulki

Jam'iyun adawa hudu na kasar Botswana sun dunkule waje daya domin tunkarar jam'iyar dake mulkin kasar wato Botswana Democratic Party , a babban zaben kasar dake tafe a shekara ta 2019.

Shugaban  Botswana Ian Khama.
Shugaban Botswana Ian Khama. (Photo : AFP)
Talla

Tun shekara ta 1966 ne dai babban jam'iyar dake mulki ke cin karen ta babu babbaka.

Sai dai kuma a shekara ta 2014 ne ta fara ganin koma baya karo na farko a lokacin da ta sami yawan kuri'u da basu zarce kashi 50%.

Ana ganin wannan rasa tabukawa na biyo bayan tafiyar hawainiya ne na tattalin arzikin kasar da kuma batun rashin ayyukan yi ga dimbin matasa.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.