Isa ga babban shafi
Gambia

Barrow ya bada umarnin sakin fursunoni 171

Shugaban kasar Gambia Adama Barrow ya bada umarnin sakin baki dayan fursunonin da ke tsare a gidajen yarin kasar, wadanda aka tsare ba tare da an gurfanar da su gaban shari’a ba saboda dalilan siyasa.

Shugaban kasar Gambia Adama Barrow a babban birnin kasar Banjul
Shugaban kasar Gambia Adama Barrow a babban birnin kasar Banjul REUTERS/Afolabi Sotunde
Talla

Barrow ya bada umarnin ne yayinda yake jaddada alkawarin da yayi na kawo karshen tauye hakkin dan adam da aka zargi gwamnatin Yahya Jammeh da aikatawa, a jawabin da ya gabatar bayan bikin kama aikinsa da ya gudana a birnin Banjul a ranar Asabar da ta gabata.

Jim kadan da bada umarnin, aka saki fursunoni 171, wadanda aka kama a zamanin gwamnatin Jammeh.

Shugaba Adama Barrow ya kuma za’a gudanar da sauye sauye a kundin tsarin mulkin kasar, zai kuma bayyana matakai na farko da za’a dauka a lokacin da zai gabatar da jawabinsa na farko ga zauren majalisar kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.