Isa ga babban shafi
Bakonmu a Yau

Matsalar Yunwa a Arewa Maso Gabashin Najeriya

Wallafawa ranar:

Yanzu haka wakilan kasashe da na kungiyoyi masu zaman kansu na gudanar da taro a birnin Oslo domin samar da tallafin kudade ga milyoyin mutane da ke fama da matsalar yunwa a yankin arewa maso gabashin Najeriya, yankin da ke fama da ayyukan Boko Haram.An fara taron ne a daidai lokacin da babban Magatakarda na MDD ke cewa yanzu haka ana bukatar sama da dalar Amurka bilyan 4 domin tunkarar matsalar yunwa a kasashen Najeriya, Somalia, Sudan ta Kudu da kuma Yemen.Majalisar dai ta ce a halin yanzu duka duka dala milyan 90 ne aka samu daga alkawullan da aka dauka.A zantawarsu da Abdoulkarim Ibrahim Shikal, Alhaji Umaru Damagaram, kwarare kan ayyukan jikai, ya bayyana mahangarsa dangane da wannan batu. 

Wata mata da yaran ta dake fama da yunwa sakamakon masifar 'yan Boko Haram.
Wata mata da yaran ta dake fama da yunwa sakamakon masifar 'yan Boko Haram. REUTERS/Afolabi Sotunde
Sauran kashi-kashi
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.