Isa ga babban shafi
Najeriya

Na ji Sauki, Ma su mugun nufi Allah ya shirye su- Inji Buhari

Shugaban  Najeriya Muhammdu Buhari ya ce zai koma bakin aikinsa makon gobe bayan ya dawo kasar yau Juma’a daga birnin London, inda ya shafe tsawon kwanaki 51 yana hutun jinya.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya shafe kwanaki 51 yana hutu a London
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya shafe kwanaki 51 yana hutu a London REUTERS
Talla

Shugaban Buhari ya samu kyakkyawar tarba a lokacin da ya ke sauka a filin jirgin Kaduna da safiyar yau Juma'a.

Bayan ya isa Abuja, Buhari ya godewa Jama’ar Najeriya dangane da Addu'o'in da suka yi masa na samun lafiya, inda ya kara tabbatar da ci gaba da gudanar da mulkinsa bisa gaskiya da amana.

"Ina shaidawa Jama'a cewa gani a gida na ji sauki, Alhamdulillahi", a cewar Buhari.

Wakilinmu daga fadar shugaban kasar a Abuja Kabiru Yusuf ya ce Buhari ya tabbatar da cewa zai koma bakin aiki sabanin wasu rahotannin da ke cewa mataimakinsa Farfesa Yemi Osibanjo zai ci gaba da mulki har ya murmure.

01:30

Na ji Sauki, Ma su mugun nufi Allah ya shirye su- Inji Buhari

Kabir Yusuf

Kakakinsa Femi Adeshina ya tabbatar da a Twitter cewa Buhari zai sanar da Majalisa dawowarsa kamar yadda tsarin doka ya tanadar domin ci gaba da aikinsa na shugaban kasa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.