Isa ga babban shafi
Sierra leone

Wani Fasto a Saliyo ya tsinci dami a kala

Wani Limanin addinin Kirista a Saliyo ya tsinci dami a kala, abin da ake ganin zai sauya rayuwarsa har abada, bayan ya tono lu’ulu’un da nauyinsa ya kai Carat 709 wanda aka bayyana cewar yana daga cikin irinsa mafi girma a duniya. 

Lu'ulu'u mai nauyin Carat 706 da Fasto Emmanuel Momoh ya tono a Saliyo
Lu'ulu'u mai nauyin Carat 706 da Fasto Emmanuel Momoh ya tono a Saliyo Sierra Leone State House
Talla

Faston mai sunan Emmanuel Momoh ya tsinci lu’u lu’un ne a lokacin aikin tono madanai a yankin Kono da ke gabashin kasar

Lu’u Lu’un da ba a kai ga sanin darajar kudinsa ba, ya kasance na 10 mafi girma da aka taba hakowa a duniya, kuma mafi girma da aka taba ganowa a Saliyo tun a shekarar 1972, a lokacin da aka tono wani mai maunin carat 969.

A lokacin karbar lu’u lu’un, shugaban kasar Saliyo Ernest Bai Karoma ya yi murna da godiya kwarai da gaske ga mutanensa da ba su yi fasa-kaurin lu'ulu'un ba daga kasar, kasancewar kasar na da tarihin nuna rashin gaskiya.

Shugaban ya kuma bayyana cewa za a siyar da shi ta hanyar da kowa zai amfana da shi a kasar da ta yi fice wajen arzikin ma'adanin lu'ulu'u.

A cikin watan Mayu ake saran kai lu’unlu’un Hong Kong don cinikin sa, da ake kwatatan kudin Carat guda da Dala miliyan 2 zuwa miliyan 3 da dubu dari shida.
 

Cinikin lu’ulu’u a baya na daga cikin abin da ya janyo yakin basasar da aka shafe shekaru ana yi, a lokacin da kungiyoyin 'yan tawaye suka yi musayar su da makamai a Saliyo.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.