Isa ga babban shafi
MDD-DRC

An gano wasu kaburbura makare da mutane a Congo

Majalisar Dinkin Duniya ta ce masu bincike sun gano wasu kaburbura makare da gawarwakin mutane a yankin Kasai na Jamhurriyar Demokradiyar Congo da ke fama da tashe-tashen hankula.

An gano manyan kaburburan mutanen da aka kashe a yankin Kasai na Jamhuriyar Demokradiyar Congo
An gano manyan kaburburan mutanen da aka kashe a yankin Kasai na Jamhuriyar Demokradiyar Congo REUTERS/Damir Sagolj
Talla

A cewar wani babban jami’in Hukumar Kare Hakkin bil’adama ta Majalisar Dinkin Duniya Jose Maria Aranaz, sun gana da hukumomin Jamhuriyar Congo in da suka yi musayar bayanai da suka shafi kaburburan da aka gano a yankin na Kasai.

Jami'in ya ce ba za su iya tantance alkaluman gawarwakin a yanzu ba, amma dai kaburburan sun haura alkaluman da aka sani a can baya.

A nasu bangaren, mahukuntan Congon ta bakin kakakin gwamnatin kasar Lambert Mende, sun amince da gano sabbin kaburbura fiye da uku makare da gawarwakin, yayin da ake ci gaba da bincike don gano asalin mamatan da kuma wadanda suka kashe su.

Rikici dai ya barke a yankin na Kasai a watan Augustan bara bayan jami’an gwamnati sun kashe wani shugaban kabilar yankin mai suna Jean Pierre Mpandi, lamarin da ya haifar da tashin hankalin da ya kai ga rasa rayukan mutane akalla 400.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.