Shirin al'adunmu na gado na wannan makon tare da Abdurrahman Gambo Ahmad ya tattauna ne kan barazanar bacewa da wasan langa ke fuskanta duk da tsohon tarihin da ya ke da shi a kasar Hausa. A cikin shirin za ku ji yadda dattijai da suka haura shekaru 70 ko kuma 80 suka gudanar da wasan Langa a lokacin kuriciyarsu. Sannan za ku ji yadda matasan yau suka yi watsi da al'adar ta malam Bahaushe.
Sauran kashi-kashi
-
Koken Jama'a a kan yadda hukumomi ke yi wa abubuwan tarihi rikon sakainar kashi
Shirin al'adun gargajiya na wannan mako ya yi duba ne a kan yadda Jama'a ke koken game da rikon sakainar kashi da hukumomi ke yi wa abubuwan tarihi, kamar Makon jiya yau ma shirin ya yi tattaki ne har Kanon Dabo da ke tarayyar Najeriya, inda ya tattauna da shugaban kwamitin raya Al'adun Gargajiya na Majalisar dokokin Jihar, Hon. Sarki Aliyu Daneji.Ku latsa alamar sauti don jin yadda shirin ya kasance....21/05/202410:08 -
Yadda Maza da Mata suka rungumi sana'ar Rini a Kano da ke Najeriya
Shirin al'adun gargajiya na wannan mako ya yi tattaki ne har Kanon Dabo da ke tarayyar Najeriya, inda ya yi duba a kan yadda Maza da Mata suka rungumi sana'ar Rini a Karofin Kofar Mata wadda ke da dogon Tarihi.Shirin ya samu zarafin tattauna wa da Baballiya Hamisu, wanda shi ne mai magana da yawun Marinar ta Kofar Mata.14/05/202410:02 -
Tasirin masu sarautar gargajiya wajen inganta tsaro a yankunansu
A sakamakon gyaran da aka yi wa kundin tsarin mulkin Nigeria na 1976, aka tsame hannun sarakunan gargajiya a kasar cikin sha’anin kula da harkokin tsaro da harkokin shari’ah da kuma batun tara haraji a cikin al’ummarsu.Hakan ne ya sanya Sarakuna duk da kasancewarsu iyayen kasa, suka koma gefe inda suka zamo ‘yan kallo kan wadannan al’amura.05/03/202410:02 -
Yadda sana'ar rini ke bacewa sannu a hankali a arewacin Najeriya
Shirin 'Al'adun Gargajiya' na wannan makon tare da Abdullahi Issa ya maida hankali ne kan bacewar sanar gargajiya ta rini a jihar Kano dake arewacin Najeriya, kafin daga bisa shirin ya leka Maradi dake jamhuriyar Nijar.14/11/202310:19 -
Bafaranshiya ta lashe kyautar iya gasa biredi ta duniya
Shirin Al’adun mu na gado tare da Abdoulaye Issa a wannan makon, ya tabo batun kyautar da matashiya 'yan Farsans ta lashe, inda ta zamo ta daya a duniya a wannan shekarar wajen iya gasa biridi. Tarihi dai ya nuna wannan ne karo na faro da mace ta taba lashe wannan kyauta.31/10/202310:31