Isa ga babban shafi
Najeriya

Shekarau da Goje sun nisanta kansu da kisan Sheikh Ja’afar

Tsohon gwamnan Gombe Sanata Danjuma Goje da tsohon gwamnan Kano Malam Ibrahim Shekarau sun nisanta kansu da kisan mashahurin malamin addini Islama Sheikh Ja'afar Mahmud Adam da aka kashe yana bada sallah a Kano.

Malam Ja'afar Mahmud Adam
Malam Ja'afar Mahmud Adam youtube
Talla

Rundunar ‘Yan Sandan Najeriya ta ce ta samu wasu takardu da ke alakanta tsohon Gwamnan Kano Ibrahim Shekarau da kashe Sheikh Malam Ja’afar a dirar mikiyar da jami’anta suka yi wa gidan Sanata Danjuma Goje.

Amma Sanata Goje ya shaidawa RFI Hausa cewa wannan wani yunkuri ne na ba ta masa suna.

“Ni ban san wannan takardar ba, ban ganta ba, ban san da zamanta ba”, a cewar Goje.

Tsohon gwamnan na Gombe ya bukaci ‘Yan sanda su fito su fadawa ‘Yan Najeriya wanda ya kashe Malam Jafar amma ba shafa masa kashin kaji ba.

Shi ma a nasa bangaren, Malam Ibrahim Shekarau ya karyata zargin kisan Malamin a lokacin da yana gwamnan Kano.

Kakakinsa Ghali Sadik ya ce wannan tsohon zance ne da aka manta a Kano bayan binciken farko da ‘Yan sanda suka gudanar a 2007, lokacin da aka bi masallatai ana raba takardar da ke zargin Shekarau nada hannu a kisan Sheik Ja'afar.

A cewarsa, watakila takardar da aka rarrabawa mutane a Kano ce a 2007 ‘Yan sanda suka samu a gidan Sanata Goje.

A ranar 13 ga Afrilu aka harbe Malam Jafar yana jagorantar Sallar Asuba a Kano, kuma har yanzu ba a gano wadanda suka kashe shi ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.