Isa ga babban shafi
Najeriya

An kai hari Jami’ar Maiduguri

Wasu ‘Yan kunar bakin wake sun kai hare haren bama bamai a ciki da wajen Jami’ar Maiduguri, inda rahotanni suka ce daya daga cikin jami’an Jami’ar ya mutu sannan kuma biyu sun samu raunuka.

An tsaurara tsaro a Borno a ranar Sallah
An tsaurara tsaro a Borno a ranar Sallah Reuters/Akintunde Akinleye
Talla

Rundunar ‘yan sandan jihar Borno ta ce wasu ‘yan kunar bakin wake uku ne suka kai hari kan jami’an tsaron da ke jami’ar Maiduguri a cikin daren jiya Lahadi da ake bikin Sallah.

Maharan wadanda mata ne dukkaninsu sun mutu, inda daya ta tayar da bom din a cikin Jami’ar, daya kuma jami’an tsaro suka harbe ta a lokacin da ta ke kokarin shiga jami’ar.

Mai maigana da yawun rundunar ‘yan sanda a Jihar ta Borno DSP Victor Isuku da ya tabbatar da faruwar lamarin, ya ce an tayar wani bom wata unguwa da ke birnin Maiduguri a ranar Sallah.

‘Yan Boko Haram dai sun sha kai hare hare a Jami’ar Maiduguri.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.