Isa ga babban shafi
Nijar

Alfaga ya samu kyakkyawar tarba a Nijar

Zakaran wasan Taekwando na duniya Issoufou Alfaga Abdoulrazak na kasar Nijar ya samu kyakkawar tarba bayan ya sauka kasar a jiya inda dubban mutane suka tarbe shi a Yamai bayan ya lashe zinari a gasar duniya da aka gudanar a Koriya ta Kudu.

Dan Nijar Issoufou Alfaga Abdoulrazak zakaran Taekwondo na duniya
Dan Nijar Issoufou Alfaga Abdoulrazak zakaran Taekwondo na duniya twitter
Talla

Ya isa fadar shugaban kasa a Yamai inda ya gana da shugaba Mahamadou Issoufou

Alfaga ya samu kyautar kudi CFA miliyan 20, kwatankacin dala dubu 41 daga gwamnatin Nijar. Sannan an karrama shi da kyautar lambar yabo mafi girma ta kasar Nijar.

Alfaga dai ya fito da kimar Nijar a idon duniya, a wasan Taekwando.

Akwai biki na musamman da aka gudanar a Yamai domin Alfaga wanda ya samu halartar Firaminista Biji Rafini.

Alfaga ya lashe zinarin ne bayan ya doke dan wasan Birtaniya Mahama Cho a wasan karshe da suka fafata a ranar 29 ga Yuni a Koriya ta kudu.

A bara Alfaga ya lashe wa Nijar azurfa a Taekwando inda ya zo matsayi na biyu a wasannin Olympics da aka gudanar a Brazil.

Shi ne dan wasa na biyu da ya lashewa Nijar kyauta a wasannin Olympics bayan dan dambe Issaka Dabore da ya lashe tagulla a 1972 a Munich.

Alfaga ne zakaran Afrika wanda ya lashe zinari a wasannin Afrika da aka gudanar a Brazzaville.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.