Kotun fasalta kundin tsarin mulkin Nijar ta yi watsi da sabon kundin zaben da majalisar dokoki ta amince da shi. Inda ta bayyana soke wasu kudurori dokar zaben da dama saboda a cewar kotun sun saba wa kundin tsarin mulkn. Daga cikin ayoyin da kotun ta yi watsi da su har da wadda ke cewa idan mutum ya aikata laifi amma ya gudu zuwa waje sannan aka yanke masa hukunci, to sam ba zai iya tsayawa takara ba, da kuma wani kuduri da ke bai wa jam’iyyun siyasa karin lokaci domin yin gyara idan kotu ta gano cewa akwai kura-kurai a cikin takardun ‘yan takarar, abinda ta ce ba zai yiyu ba. Abdoulkarim Ibrahim Shikal ya zanta da Honarabul Mourtala Mahamouda, daya daga cikin ‘yan majalisar da suka amince da kundin.
Sauran kashi-kashi
-
Attahiru Bafarawa kan shirin ƴan adawa na tinkarar jam'iyya mai mulki a 2027
A Najeriya, yanzu haka wasu daga cikin manyan ‘yan adawar ƙasar cikin su harda wadanda suka tsaya takarar zaɓen shekarar 2023 sun fara tintibar juna domin tsara yadda za su tinkari jam’iyya mai mulki a zaɓe mai zuwa. Rahotanni sun ce akwai yiwuwar kafa wata sabuwar jam’iyya domin kalubalantar gwamnati mai ci.Dangane da wannan yunkuri, Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da tsohon Gwamnan Jihar Sokoto, Alhaji Attahiru Dalhatu Bafarawa. Kuna iya latsa alamar sauto domin sauraren hirar.15/05/202403:18 -
Farfesa Kailani Muhammed a kan batun satar danyen mai a Najeriya
Hukumomin Najeriya sun ce sun kama jiragen ruwa 14 da ake satar danyan man fetur a Neja Delta tsakanin watan Janairun wannan shekara zuwa karshen watan Maris.Rundunar dake aikin samar da tsaro a Jihar Rivers tace wannan bai hada da kananan jirage 90 da kuma mutane 74 da ta kama ba, wadanda ke yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa.Dangane da wannan matsala, Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da Farfesa Kelaini Muhammed, masani a kan harkar gas da man fetur, kuma ga yadda zantawar su ta gudana.14/05/202403:31 -
Kwamandan MNJTF Janar Ibrahim Sallau kan nasarar su a yankin tafkin Chadi
Rundunar hadin gwuiwa da ke yaƙi da mayakan Boko Haram a Tafkin Chadi da ake kira MNJTF ta sanar da kashe mayaka 299 a cikin watanni 10 da suka gabata da kuma samun wasu 273 da suka mika kansu cikin lumana. Kwamandan rundunar Manjo Janar Ibrahim Sallau Ali ya bayyana haka ga Babban Editan sashin Hausa Bashir Ibrahim Idris a tattaunawar da suka yi ta wayar tarho bayan ya kwashe watanni 10 yana jagorancin rundunar mai cibiya a kasar Chadi.Ku latsa alamar sauti domin sauraren zantawar su.09/05/202406:33 -
Farfesa Dicko Abdurrahmae kan zaben Chadi
Yau Litinin aka bude rumfunan zabe a kasar Chadi, don zaben shugaban kasa da zai kafa sabuwar gwamnatin Chadi da ta kasance karkashin mulkin soji na tsahon shekaru 3.06/05/202403:30 -
Farfesa Umar Pate: Kan Ranar 'Yancin 'Yan Jarida ta Duniya
Yau ce Majalisar Dinkin Duniya ta ware a matsayin ranar ‘yan jaridu ta duniya, inda ake nazari a kan kalubalen da ma’aikatan jarida ke fuskanta da kuma lalubo hanyoyin inganta aikin.03/05/202403:41