Isa ga babban shafi
Mali

Rikicin Mali na yaduwa zuwa Burkina da Nijar

Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargadin cewar rikicin kasar Mali na yaduwa zuwa kasashen Burkina Faso da Jamhuriyar Nijar, ganin yadda ake samun hare haren ‘yan ta’adda akan iyakokin kasashen da ke makwabta.

Sojojin Mali da ke fada da 'yan ta'adda a arewacin kasar
Sojojin Mali da ke fada da 'yan ta'adda a arewacin kasar PHILIPPE DESMAZES / AFP
Talla

Jakadan Majalisar na musamman a Yankin Afirka ta Yamma, Mohammed ibn Chambers ya bayyana haka, lokacin da ya ke gabatar da rahoto a gaban kwamitin Sulhu.

Chambers ya ce yanzu haka hare haren da ake samu akan iyakokin na matukar illa ga rayuwar jama’a na yau da kullum.

Jami’in ya ce yanzu haka masu safarar kwayoyi da mutane da kuma makamai na amfani da halin da ake ciki wajen cin karen su babu babbaka.

A watan jiya kwamitin Sulhu ya amince da kudirin kafa rundunar tsaro mai dauke da mutane 5,000 domin magance matsalar.

Kasashen yankin sahel guda biyar sun amince suka kafa runduna ta musamman domin yakar ta’addanci.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.