Isa ga babban shafi
Najeriya

‘Yan Neja Delta sun ba gwamnatin Najeriya wa’adi

Kungiyar Dattawan Yankin Neja Delta a kudancin Najeriya ta ba Gwamnatin kasar wa’adin zuwa ranar 1 ga watan Nuwamba ta biya bukatunta ko kuma ta fice daga tattaunawar samun zaman lafiya da suke yi tsakaninsu.

Wani gidan Mai da ke yawo na Kamfanin NNPC na Najeriya  a tsakiyar ruwa yankin Neja Delta
Wani gidan Mai da ke yawo na Kamfanin NNPC na Najeriya a tsakiyar ruwa yankin Neja Delta REUTERS
Talla

Tawagar shugabannin a karkashin Chief Edwin Clark ta ce sun ba Gwamnati bukatun 16 cikinsu har da yaki da talauci a Yankin domin kawo karshen hare haren da ake kai kan bututun mai, amma gwamnati ta kasa aiwatarwa.

A watan Nuwamban bara ne shugabannin yankin na Neja Delta suka mikawa shugaba Buhari bukatunsu 16, matakin da ya takaita hare haren tsagerun yankin akan kadarorin gwamnati.

Bukatun sun hada da dawo da dawo da manyan ofisoshin kamfanonin mai zuwa kudancin kasar da kara ware kudaden tallafi domin ci gaban yankin.

Mista Clarke ya ce za su fice tattaunawar idan har gwamnati ta gaza cimma bukatunsu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.