Shugaba Paul Kagame Ya Lashe Zaben Shugaban Kasar Rwanda
Shugaban kasar Rwanda Paul Kagame ya lashe zaben shugabancin kasar inda zai fara wa'adi na uku bayan alkaluman sakamakon zaben na nuna ya sami yawan kuri'u kashi 98% na yawan kuri'u da aka jefa.
Wallafawa ranar:
Kashi 80% na yawan kuriun ne dai aka kirga ya zuwa yammacin jiya Asabar kamar yadda Hukumar zaben kasar ta sanar.
A cewar Hukumar zaben Kashi 97% na jimillan masu jefa kuri'u kusan miliyan bakwai suka jefa kuri'a as yayi zaben na Lahadi.
Shugaban Hukumar Zaben Kalisa Mbanda ya gaskata cewa Shugaban kasar Paul Kagame yayi gagarumin nasarar lashe zaben.
Paul Kagame mai shekaru 59 ya kwashe shekaru 17 yana mulkin kasar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu