Isa ga babban shafi
Uganda

'Yan gudun hijirar Sudan ta kudu milyan daya na Uganda

Majalisar dinkin duniya ta ce adadin ‘yan gudun hijirar da suka tsallaka Uganda daga Sudan ta kudu sun haura mutum miliyan guda, a dai dai lokacin da ake ganin babu alamun kawo karshen rikicin kasar da ke kara yawan rikicin ‘yan gudun hijira cikin gaggawa a duniya.

Rikici tsakanin Shugaba Salva Kiir da Riek Machar ya haddasa yakin basasa kusan shekaru hudu a sudan ta kudu
Rikici tsakanin Shugaba Salva Kiir da Riek Machar ya haddasa yakin basasa kusan shekaru hudu a sudan ta kudu Reuters
Talla

A cewar hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya yakin basasar Sudan ta kudu da yanzu haka ya doshi shekaru 4 ana tafkawa, ya tilastawa al’ummar kasar akalla dubu daya da dari takwas galibi kananan yara da mata ficewa daga kasar kowacce rana tun daga bara, don samun matsugunai a kasashen ketare.

Haka kuma kimanin mutum milyan daya na al’ummar kasar yanzu haka na zaune a Uganda kasa mafi talauci a kasashen duniya, inda suke jiran shaguna ko kuma wasu aikace-aikace da za su tallafa musu iya ciyar da kansu.

Babban jami’in hukumar kula da ‘yan gudun hijira a arewacin Uganda Bik Lum ya ce a kullum daruruwan ‘yan gudun hijira na kwararowa zuwa sansanin wanda ke dauke da sama da mutum dubu dari biyu da saba’in, babu kuma tabbacin ranar da za a iya cewa itace karshen zuwansu.

Tun a watan Disambar shekarar 2013 ne Sudan ta kudu ta fada yakin basasa shekaru biyu bayan samun ‘yancin kai, inda shugaba Salva Kiir ya zargi mataimakinsa Riek Machar da kitsa yunkurin juyin mulki.

Lamarin daya juye zuwa rikicin kabilanci a shekarar 2015 bayan watsi da yarjejeniyar zaman lafiya tsakanin bangarorin biyu, inda kawo yanzu ake ci gaba da asarar rayuka baya ga tilastawa miliyoyin al’ummar kasar barin matsugunansu don tsira da rayukansu.

Rahotan ya kuma bayyana cewa akwai dubban al’ummar Sudan ta kudun da yanzu haka ke rayuwa a kasashen Sudan da Ethiopia da Kenya da Jamhuriyyar Demokradiyyar Congo da kuma Afrika ta tsakiya, inda kuma mutum miyan biyu a cikin kasar suka rasa matsugunansu.

Hukumar kula da ‘yan gudun hijirar ta ce tana bukatar dala milyan 674 cikin shekarar nan kadai don tallafawa ‘yan gudun hijarar amma kawo yanzu kaso biyar cikin adadin kadai ta biya samu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.