Isa ga babban shafi
Najeriya

Boko Haram: Birtaniya za ta ba Najeriya taimakon fam miliyan 200

Gwamnatin Birtaniya ta yi alkawalin ba Najeriya taimakon Fam miliyan 200 a cikin shekaru 5 masu zuwa domin magance matsalar da Boko Haram ta haifar.

'Yan gudun hijirar rikicin Boko Haram a Najeriya
'Yan gudun hijirar rikicin Boko Haram a Najeriya TRF-Kieran Guilbert
Talla

Sakataren harkokin wajen kasar Boris Johnson ya bayyana haka lokacin da ya ziyarci Maiduguri domin ganewa idonsa halin da ake ciki.

Johnson ya ce ya gana da mutanen da rikicin Boko Haram ya tagayyara a Maiduguri, kuma wasu daga cikinsu suna dauke da harbin bindiga da raunin bam, sannan kuma ya ga yadda rikicin ya raba dubban mutane da gidajensu.

Sakataren ya ce tallafin kudin da Birtaniya za ta bayar za a yi amfani da shi wajen ciyar da ‘yan gudun hijira miliyan daya da rabi da kula da lafiyar yara sama da 120,000 da kuma taimakawa wasu yara 100,000 samun ilimi.

Sannan sojojin Birtaniya za su ci gaba da taimakawa jami’an tsaron Najeriya wajen yakar ta’addanci, bayan horar da sama da 28,000.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.