Isa ga babban shafi
Nijar

Mutane 44 suka mutu a ambaliyar ruwa a Nijar

Gwamnatin Kasar Nijar ta ce mutane 44 suka mutu sakamakon ambaliyar ruwa da aka samu tsakanin watan Yuni zuwa yau, yayin da sama da 70,000 suka rasa muhallinsu.

Ambaliya ta yi barna a Nijar a bana
Ambaliya ta yi barna a Nijar a bana BOUREIMA HAMA/AFP
Talla

Daraktan kare jama’a Boubacar Bako wanda ya bada alkaluman ya ce gidaje 9,523 suka rushe, yayin da matsalar ta shafi mutane 77,225.

Bako ya ce 41 daga cikin wadanda suka mutu gini ne ya fada akansu, yayin da 3 kuma suka nutse a ruwa.

Daraktan ya ce a birnin Yamai kawai mutane 17 suka mutu, akasarinsu yara kanana.

Sannan ambaliyar ta rusa gidaje sama da 8,000 da suka kunshi na ginin zamani da kuma na kasa.

A makon jiya hukumomin Nijar suka bukaci dubban mazauna birnin Yamai da su kauracewa gidajensu musamman yankunan da ke fuskantar barazana.

Ambaliyar ruwa a Najeriya babbar matsala ce da ake samu duk shekara, inda ko a bara kusan mutane 50 suka mutu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.