Chadi
Cutar amai da gudawa ta kashe mutane 52 a Chadi
Hukumomin kiwon lafiya a kasar Chadi sun sanar da barkewar cutar amai da gudawa wadda tuni ta lakume rayukar mutane 52, bayan ta kama mutane 312.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Talla
Sakataren ma’aikatar lafiyar kasar Hamid Djabar, ya ce tuni suka kafa kwamitin gaggawa wanda zai yi aikin dakile yaduwar cutar, tare da aiki da hukumar UNICEF da kuma jami’an kungiyar agaiji ta Medicins Sans Frontiers.
A shekarar 2011 an samu barkewar irin wannan cutar, mutane 17,200 suka kamu, yayin da sama da 450 suka mutu.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu