Isa ga babban shafi
Guinee

Hukumomin Guinee sun dakatar da wani gidan rediyo

Gwamnatin kasar Guinea ta dakatar da wani gidan rediyo daga gudanar da aikin sa saboda kokarin da ya yi na hira da shugaban malaman makarantun dake yajin aiki.Shugaban gidan rediyo Alpha Fady Diallo dake garin Labe, ya ce suna gab da fara hira da shugaban malaman ne jami’an tsaro suka kutsa kai, inda suka katse shirin rediyon.

Wani gidan Rediyo mai suna Espace Fm a kasar Guinee
Wani gidan Rediyo mai suna Espace Fm a kasar Guinee Radio Espace FM
Talla

Gwamnan Labe, Sadou Keita ya ce an dakatar da shirin rediyon ne na wani lokaci amma ba rufe shi akayi ba.

Tuni aka kama malamai da dama da suka shiga zanga zangar adawa da kin karin albashin da gwamnati ta ki yi, yayin da matasa biyu suka rasa rayukan su.

Da dama daga cikin kungiyoyi masu zaman kan su na ci gaba da yi kira zuwa hukumomin kasar don gani sun daina yi katsan landan ga harakokin manema labarai na wannan kasa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.