Isa ga babban shafi
Libya-Bakin-haure

Libya ta amince da shirin kwashe bakin da ake cin zarafin su

Shugaban Faransa Emmanuel Macron, wanda ke zantawa da Radio France International da kuma tashar talabijin France 24 a gefen taron kasashen Turai da na Afrika da ke gudana a birnin Abidjan na kasar Ivory Coast, ya ce gwamnatin Libya ta amince da shirin kwashe bakin da ake cin zarafin su.

Shugaban Kasar Faransa Emmanuel Macron
Shugaban Kasar Faransa Emmanuel Macron RFI
Talla

Matakin ya biyo bayan kiran da shugaban kasar Cote d’Ivoire Alasane Ouattara ya yi na amfani da duk wani matakin da ya da ce domin kawo karshen bauta da azabtarwar da ake yiwa bakin.

Shugaba Macron ya ce shugabannin kasashen Faransa da Jamus da Chadi da Nijar da kuma wasu kasashe 4 sun amince a kaddamar da wani shirin gaggawa na kwashe baki daga kasar.

Macron ya ce Firaministan Libya Fayez Sarraj ya ce gwamnati zata binciko sansanonin da ake cinikin bayin domin hukunta su.

00:56

Saurari abin da Macron ke cewa a kan Libya

RFI

Wakilan Majalisar Dinkin Duniya da kungiyar kasashen Turai da Afirka sun bayyana aniyar kara taimakawa kungiyar da ke kula da kaurar baki domin kwashe bakin a kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.