Isa ga babban shafi
Togo

'Yan kasar Togo sun sha alwashin ci gaba da zanga-zanga

Dubban ‘yan Togo sun sake fantsama kan titunan babban birnin kasar Lome, domin ci gaba da zanga-zangar kawo karshen mulkin shugaba Faure Gnassingbe, da ya shafe sama da shekaru 15 yana rike da shi.

Wasu daga cikin masu zanga-zanga a kasar Togo da suka fantsama a titunan babban birnin kasar Lome.
Wasu daga cikin masu zanga-zanga a kasar Togo da suka fantsama a titunan babban birnin kasar Lome. MATTEO FRASCHINI KOFFI / AFP
Talla

Tun daga watan Agustan da ya gabata ne, dubban ‘yan kasar, bisa jagorancin gamayyar jam’iyyun adawa, suke gudanar da irin wannan zanga-zangar kusan a kowane mako.

Sai dai har yanzu duk da kokarin shiga tsakani da shugabannin kasashen nahiyar Afrika ke yi, an gaza samun dai daito a siyasar kasar, inda bangaren 'yan adawa suka dage kan lallai sai an kawo karshen mulkin sama da shekaru 50 da iyalan gidan Gnassingbe suka shafe suna yi a kasar.

Sai da janar Gnassingbe Eyadema, wato mahaifin shugaba mai ci, ya shafe, shekaru 38 yana mulkar Togo kafin daga bisani, Faure Gnassingbe ya dora daga shekarar 2005, bayan mutuwar mahaifin nasa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.