Isa ga babban shafi
Benin- Nijar

Za'a fara aikin samar da layin jirgin kasa tsakanin Nijar da Benin

Shugabannin kasashen Nijar da Benin sun amincewa kamfanin kasar China shiga a dama da su wajen gagarumin aikin shimfida layin dogo da zai samarda sufuri tsakanin kasashen yankin da yawa.

Shugaba Issoufou Mahamadouyayi da yake jawabi wajen wani taro a shekara ta 2016
Shugaba Issoufou Mahamadouyayi da yake jawabi wajen wani taro a shekara ta 2016 rfi
Talla

Shugaban Nijar Muhammadu Isufu ya fadawa taron manema labarai a Yammai bayan ganawa da takwaransa na Benin cewa sun amince kuma suna daukan matakan da suka dace don tabbatar da wannan aiki.

A watan jiya Gwamnatin Benin ta umarci wani kamfaninta Petrolin da kuma kasaitaccen kamfanin Faransa Bollore da su janye daga aikin shimfida layukan dogo domin kamfanin kasar China ya ci gaba da aikin.

Tun a shekara ta 2008 kasar Nijar da Benin suka kaddamar da fara aikin gina layin jirgin kasa mai tsawon kilomita 740 da zai hada Cotonou da Yammai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.