'Yansanda sun tarwatsa 'yan Shi'a masu zanga-zanga a Abuja
Jami'an 'Yansanda a Abuja babban birnin Najeriya sun tarwatsa wani dandazon mabiya Shi'a da suka shirya zanga-zangar adawa da ci gaba da rike jagoransu Sheikh Ibrahim Zakzaky da gwamnatin kasar ke ci gaba da yi tsawon lokaci.
Wallafawa ranar:
Wannan dai ba shi ne karon farko da Mabiya na Shi'a ke gudanar da makamanciyar zanga-zangar ba, inda a lokuta da dama jami'an tsaro kan tarwatsa su.
Mabiyan dai na bukatar lallai gwamnatin Najeriyar karkashin shugaba Muhammadu Buhari ta mutunta umarnin kotu wajen sakin Jagoran na su Ibrahim Yakubu Zakzaky da ta ke rike da shi kusan shekaru biyu.
Jami'an tsaron sun yi amfani da hayaki mai sanya hawaye kan dandazon mabiyan na Shi'a don tarwatsa su.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu