Isa ga babban shafi
Najeriya

An yi nasarar magance annobar zazzabin Lassa a Najeriya

Hukumar lafiya ta Duniya WHO ta ce anyi nasarar shawo kan Cutar Lassa waddda bera ke yadawa a Najeriya. A cewar WHO a makwanno 6 da suka gabata ana samun raguwar cutar yayinda a yanzu ake da mutane kalilan da ke fama da cutar a kasar wadda ta yi fama da barkewar cutar a baya.

Kusan a duk lokacin da aka samu bullar cutar ta Lassa a Najeriya akan fuskanci asarar dimbin rayuka.
Kusan a duk lokacin da aka samu bullar cutar ta Lassa a Najeriya akan fuskanci asarar dimbin rayuka. PHILIPPE LOPEZ / AFP
Talla

Hukumar Lafiyar ta ce an dai samu barkewar Cutar ta Lassa ne a Najeriya, kuma lallai ne a ci gaba da daukar matakin magance watsuwarta.

A makon karshe da aka samu rahoton halin da ake ciki dangane da Cutar ta Lassa da ya kasance karshen watan da ya gabata, an samu labaran wasu mutane da suka kamu da Cutar.

A wannan Shekarar dai an samu tabbatar da samun rahotannin kamuwa da Cutar akalla 423 ciki kuwa har da mutane 106 da suka mutu, amma an samu bayannai akan yadda Cutar ke raguwa a dukkanin fadin kasar a cikin makonni 6 da suka gabata abinda ya sa aka samu kasa ga adadin da za’a iya bayyanawa a matsayin Annoba, idan aka yi la’akari da yanda aka samu barkewarta a baya.

Daraktan yanki mai kula da ayyukan agajin gaggawa na Nahiyar Afruka a Hukumar lafiya ta majalisar dinkin Duniya Dr Ibrahim Soce Fall, ya ce ya zama wajibi a taya Najeriya murnar wannan nasarar da ta samu amma kuma wannan bas hi zai sa su dagawa aikin nasu kafa ba.

Ya ce dole su yi amfani da darussan da suka samu a aikin kawar da Cutar a tarayyar Najeriya domin tinkarar kasashen da ke fuskantar barazanar yiyuwar kamuwa da Cutar nan gaba.

Inji Daraktan Hukumar lafiya ta majalisar dinkin Duniya za ta ci gaba da taimaka wa Najeriya wajen ci gaba da ayyukan dakushe Cutar baki daya, musamman lura da cewar ma’aikatan lafiya 37 ne aka bada labarin sun kamu da cutar kuma 8 daga cikinsu suika mutu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.