Paul Kagame ya gana da Emmanuel Macron
Shugaban kasar Rwanda Paul Kagame ya gana da Shugaban Kasar Faransa Emmanuel Macron a fadar Elysee, a kokarin sun na bunkasa hulda tsakanin kasashen biyu, bayan shekaru 20 na zanga zangar kisan kare dangi a Rwanda da gwamnatin Rwanda ta zargi Faransa da taimakawa wajen kisan yan kasar ta.
Wallafawa ranar:
Shugaban kasar Rwanda dake ci gaba da fuskantar suka daga wasu yan kasar ,ya bayyana fatan sa na samu goyan bayan Faransa ga takarar Ministan Rwanda a kujerar Shugabancin kungiyar dake amfani da harshen Faransanci.
Paul Kagame yayi amfani da wannan dama domin ganawa da wasu Shugabanin kamfanonin sadarwa na Facebook a lokacin cin abinci bisa gayatar Shugaban Faransa, Rwanda na daga cikin kasashen Afrika da suka samu ci gaba na musaman ta fuskar ingata sashen sadarwa na intanet.
A ganawa da Shugaban kasar ta Rwanda Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya bayyana cewa zai halarci taron kungiyar Africa a Mauritania, taron da zai gudana a watan Mayu na wannan shekara.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu