Isa ga babban shafi
Najeriya

Matatun mai biyu zasu soma aiki a Najeriya a shekara mai kamawa

Gwamnatin Najeriya ta ce a shekara mai kamawa wasu kananan matatun mai biyu zasu soma aiki a yankin Naija Delta.

Daya daga cikin matatun mai a Najeriya
Daya daga cikin matatun mai a Najeriya News Nigeria
Talla

Cikin sanarwar da ya rabawa manema labarai a Abuja Ministan albarkatun man Najeriya Ibe Kachikwu, akwai kuma wasu karin kananan matatun man guda takwas da za a samar domin aiki a daya yankin na Naija Delta domin saukaka samar da tataccen man fetur a sassan kasar.

Ministan ya ce binciken da aka yi ya nuna cewa, cikin shekaru 15 da suka gabata, an baiwa yankin Naija Delta mai arzikin mai sama da dala biliyan 40 domin samar da ababen more rayuwa ga al’ummar yankin da ayyukan yi, amma har yanzu kwalliya bata biya kudin sabulu ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.