Bakonmu a Yau
Mai Mala Buni kan yadda ta wakana a taron Jam'iyyar APC na kasa
Wallafawa ranar:
Kunna - 03:29
A jiya ne aka kammala zaben sabbin shuwagabannin da za su jagoranci jamiyar APC mai mulki a Najeriya na tsawon shekaru hudu masu zuwa. Sai dai duk da sabon zaben da jamiyar ta gudanar, kawunan wasu jiga-jiganta na cigaba da kasancewa a rarrabe.Wakilinmu na Muhammad Kabir Yusuf wanda aka gudanar da zaben a gaban idonsa, ya samu zantawa da sabon sakatare jamiyar na kasa, Mai Mala Buni kan ko wane shiri suka yi wajen sake hade kan 'ya'yan jamiyar tasu?