Ali Modu mazaunin garin Dikwa kan halin da 'yan gudun hijira ke ciki
Wallafawa ranar:
Kunna - 03:30
Kungiyoyin agaji, sun yi gargadin cewa dubban mutane da rikicin Boko Haram ya tilasta wa barin gidajensu ne za su iya kamuwa da cututuka sakamakon rashin muhallai musamman a wannan lokaci da damina ta fara sauka a yankin arewa maso gabashin Najeriya.Daya daga cikin kungiyoyin da ke gudanar da ayyuykan jinkai a yankin Norvegian Refugee Council, ta ce a garin Dikwa kawai, akwai ‘yan gudun hijira sama da dubu 4 da ke kwanciya fili sakakamon rashin muhalli. Abdoulkarim Ibrahim Shikal ya zanta da wani mai suna Ali Modu, da ke zaune a garin na Dikwa, wanda ya yi masa karin bayani dangane da wadannan ‘yan gudun hijira.