Isa ga babban shafi
Kenya

Gobara ta kashe mutane 15 a kasuwar Nairobi

Gobara ta kashe mutane akalla 15 tare da raunata sama da 70 a kasuwar Gikomba da ke birnin Nairobi na Kenya kamar yadda mahukuntan kasar suka sanar.

Kasuwar Gikomba da ta kama da wuta a birnin Nairobi
Kasuwar Gikomba da ta kama da wuta a birnin Nairobi TONY KARUMBA / AFP
Talla

Jami’in gwamnati mai kula da shiyar da hadarin ya auku, Kangethe Thuku ya shaida wa manema labarai cewa, sun rasa mutane 15 a safiyar yau bayan tashin gobarar  a cikin tsakar daren da ya gabata.

Thuku ya ce, kawo yanzu ba su tabbatar da musabbabin tashin gobarar ba , amma ta fara ne daga bangaren hada-hadar itatuwa a kasuwar, yayin da kuma ta lalata kadarori da dama.

Jami’an ‘yan sanda na ci gaba da gudanar da aikin ceto a kasuwar wadda hayaki ya turukune ta.

Ko a watan Oktoban da ya gabata, sai da gobara ta tashi a wannan kasuwa, in da ta yi gagarumar barna.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.