Isa ga babban shafi
Najeriya-Zabe

Tashe-tashen hankula na barazana ga zaben 2019 a Najeriya - Amurka

Wasu kungiyoyin bunkasa dimokiradiya na kasar Amurka guda biyu da ake kira ‘National Democratic Institute’ da ‘International Republican Institute’, sun bayyana cewar tashe-tashen hankulan da ake samu a Najeriya na yi wa shirin zaben shugaban kasar da za ayi shekara mai zuwa barazana.

Kungiyoyin sun ce haren kungiyar boko haram da rikici tsakanin makiyaya da manoma a tsakiyar kasar sun yi sanadiyar hallaka akalla mutane 1,000 a cikin wannan shekarar.
Kungiyoyin sun ce haren kungiyar boko haram da rikici tsakanin makiyaya da manoma a tsakiyar kasar sun yi sanadiyar hallaka akalla mutane 1,000 a cikin wannan shekarar. http://nigeriannewsdirect.com
Talla

Tawagar kungiyoyin biyu da suka ziyarci Najeriya domin ganin shirin zaben, sun ce muddin ba’a shawo kan tashe-tashen hankulan da ake samu a jihohin kasar da dama ba, suna iya tarnaki wajen shirin gudanar da zaben mai zuwa.

Kungiyoyin sun ce haren kungiyar boko haram da rikici tsakanin makiyaya da manoma a tsakiyar kasar sun yi sanadiyar hallaka akalla mutane 1,000 a cikin wannan shekarar.

Cinikin makamai ta hanyar da bata kamata ba da kuma rashin iya dakile rikice rikice daga bangaren jami’an tsaro da kuma danganta su da Yan siyasa da shugabannin addini na dada zafafa tashin hankalin.

Kungiyoyin bayan sun bukaci tashi tsaye daga bangaren jami’an tsaro domin shawo kan matsalolin, sun kuma bayyana damuwa kan yawan yan gudun hijra da suka bar gidajen su da bukatar ganin an ba su damar kada kuri’a a zaben mai zuwa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.